Uncategorized
Masha Allahu; Dattijuwa ‘Yar Shekara 77 Ta Sauke Al’qur’ani Mai Girma A Katsina
Masha Allahu; Dattijuwa ‘Yar Shekara 77 Ta Sauke Al’qur’ani Mai Girma A Katsina
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Malama Aishatu Nuhu, Wadda Ke Zauna A Kofar Kaura, Kwalan-kwalan Cikin Garin Katsina Ta Sauke Al’qur’ani Mai Girma A Jiya Asabar.
Daya Daga Cikin Yaƴanta Aminu Dan Sarki Ya Shaida wa RARIYA Cewa Ta Kwashe Tsawon Shekara Goma Sha Biyu Tana Zuwa Makarantar Malama Usaina Babba Dake Daki Tara Cikin Garin Katsina Har Allah Ya Sanya Ta Sauke Yau.
Malama Aishatu Nuhu, Tana Da Yaya Da Jikoki Sama Da 90. Yaya Da Jikoki Sun Zo Domin Taya Murnar Samun Nasarar Sauke Al’qur’ani Mai Girma.
Allah Ya Albarkaci Abinda Aka Karanto!