Uncategorized

Labarin wani matashi a Jihar Yobe wanda ya koma rayuwa cikin ƙogon bishiyar kuka.

Labarin wani matashi a Jihar Yobe wanda ya koma rayuwa cikin ƙogon bishiyar kuka.

Muhammadu wani matashi ne a Jihar Yobe, a wani kauyen karamar hukumar Fika wanda ya hakura da rayuwa cikin garin su ya koma cikin ƙogon bishiyar kuka kimanin shekaru biyar yana rayuwa a cikin ta.

A wani hira da Mustapha Gujba ya yi da shi, Muhammadu ya ce dalilan da suka saka ya koma cikin ƙogon bishiyar kuka yace domin ya cigaba da rayuwar sa, ya ce, Allah yayi masa wata baiwa na sanin abubuwan da zasu iya faruwa cikin kwanaki ko watanni masu zuwa a cikin yawan mafarke-mafarke, amma idan ya sanar da n mutanen garinsu sai suyi masa kallon mahaukaci.

Kullum idan ya ba su labarin wani al’amuran da za su faru sai ƴan kauyen su ɗauke sa mara hankali, hakan sai ta sa ya ji ba zai iya zama cikin su ba, sai ya koma cikin ƙogon bishiyar kuka wanda yanzu haka yayi tsawon shekaru biyar yana kwana a cikin ta.
@topfans
Mustapha Moh’d Gujba Banker

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button