Uncategorized

Amarya ta rasu sa’o’i kaɗan da ɗaura aurenta a Kano Allah Kasa Annabi Muhammad S.A.W Yacece Ta Ranar Tashin Al’Qiyama….

Amarya ta rasu sa’o’i kaɗan da ɗaura aurenta a Kano Allah Kasa Annabi Muhammad S.A.W Yacece Ta Ranar Tashin Al’Qiyama….

Wata amarya, ƴyar shekara 28, mai suna Hannatu Yahaya da ke unguwar Kawon Maigari a cikin birnin Kano ta rasu sa’o’i kaɗan bayan ɗaurin aurenta.

Rahotanni sun baiyana cewa Hannatu ta rasu ne sakamakon wata rashin lafiya da ba a tabbatar da ita ba da ke da nasaba da ciwon ciki da yammacin ranar Asabar.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa ɗan uwanta, Ayyuba Yahaya, ya ce marigayiyar ba ta da wani tarihin rashin lafiya sai makonni biyu da suka gabata.

Hannatu ta auri Isyaka Yusuf a masallacin Bulama da ke Kano a ranar Asabar.

Ƙoƙarin neman ango, Isyaka Yusuf saboda martanin da ya yi ya ci tura yayin da ya ƙi cewa komai.

An yi jana’izar ta a safiyar Lahadi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button