Alhamdulillahi! Lukman LABARINA Da Matar Sa Ameena Sun Samu Ƙaruwar Ɗa Namiji……
Alhamdulillahi! Lukman LABARINA Da Matar Sa Ameena Sun Samu Ƙaruwar Ɗa Namiji……
Daga ƙarshe dai, fitaccen jarumi a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, wadda ke taka rawar Lukman a cikin shirin Labarina mai dogon zango, wato Yusuf Muhammad Abdullahi (Sasen) tare da amaryar sa Ameena Zakari Yunusa sun samu ƙaruwar haihuwar ɗa namiji, bayan watanni 9 da kwana 16 da auren su.
Ameena dai ta haifawa Yusuf Sasen santalelen ɗa namiji ne a daren ranar Litinin a wani Asibitin kuɗi na MGK da ke daura da Asibitin Koyarwa na Aminu Kano. Kuma tuni Yusuf ya yi wa jaririn huɗuba tare da sanya masa suna Muhammad Auwal.
Idan za a tuna dai, an ɗaura auren jarumin ne a ranar Asabar, 24 ga watan Disambar 2022 a cikin garin Potiskum ta Jihar Yobe da misalin ƙarfe 11.30am na safe.
Da fatan Allah Ya raya mana shi bisa turbar Addinin Musulunci. Amin.
Daga Ahmad Nagudu TV