WASU DAGA CIKIN MATASAN DA A’ISHA HUMAIRA TA BIYAWA TARA SUKA FITO DAGA GIDAN YARI
WASU DAGA CIKIN MATASAN DA A’ISHA HUMAIRA TA BIYAWA TARA SUKA FITO DAGA GIDAN YARI
Kamar yadda kuke gani cikin wannan hoto, Ayshatul humairah ce tsaye tare da wasu daga cikin ɗumbin matasan da ta yi sanadiyyar fitowarsu daga gidan gyaran hali da tarbiyya ta hanyar biya musu kuɗin tara.
Wasu daga cikin matasan sun shiga gidan yari ne a sanadiyyar ƙananan laifuffuka kamar bashi, a yayin da wasu kuma sharri aka yi musu ba ma su ne suka aikata laifin da ya jawo musu ɗauri ba.
A lokuta daban-daban Humaira ta sha ziyartar gidan yari ta kai gudunmawar kayayyakin amfanin yau da kullum gami da biyan tara ga ɗaurarru. Wasu 500,000 wasu 200,000 wasu 300,000 waɗanda duk yanzu haka sun fito suna cigaba da gudanar da sana’o’insu cikin aminci da ƴanci.
Wane fata zaku yi mata ?